By Ishaq Dabai
Gwamnan jihar Plateau Simon Lalong yayiwa gwamnatin sa garan bawul biyo bayan a jiye aiki da wasu kwamishinoni uku sukayi a ranar laraba.
Hakan yana kunshe cikin wata sanarwar da mai magana da yawun gwamnan kan harkokin yada labarai Dakta Makut Macham ya rabawa manema labarai.
Yace kwamishinonin uku na jihar Plateau sun ajiye aiki ne biyo bayan nuna wata alama ta tsayawa takarar shugaban nin kananan hukumomi kafin zabe mai zuwa da za’ayi a wata mai kamawa.
A cewar Makut wadanda suka a jiye aiki a kwai kwamishinan gidaje Barista Zulfa Bitrus, wanda ta tsaya takarar kujerar shugaban karamar hukumar Lantan ta Arewa, sai kwamishinan raya karkara da cigaban ta Alhaji Dayyabu Garba wanda ya tsaya takarar shugaban karamar hukumar Kanam, da kuma kwamishinan Ilimi mai zurfi Kakmena Goteng wanda ya nemi ya zama shugaban karamar hukumar Pankshin.
Makut ya kara da cewa kwamishinan yada labarai Honarabil Dan Manjang shine ya bayyana hakan a yayin gudanar da zaman majalissar zartarwa na jihar inda yace abin a yabawa kwamishinonin uku ne.
Gwamnan Lalong yace ya mayar da kwamishinan muhalli Mr Usman Idi zuwa ma’aikatar raya karkara da cigaban ta sannan kwamishinan Ilimi na makarantun sakandire Mrs Elizabeth Wapmuk data rike ma’aikatar Ilimin mai zurfi.
Sanarwar tace ma’aikatar gidaje sai nan gaba idan kwamishinan ayyuka na musamman Mr Jerry Werr yaje ya dubata za’ ayi nazarin wanda za’a baiwa dan maye gurbin kwamishinonin guda uku.