Majalisar dattajai ta umurci kwamitinta mai kula da harkokin cikin gida da ya fara bincike domin gano al’amuran da ke faruwa a gidajen gyaran hali a kasar.
A zaman majalisar na ranar Talata sun umurci kwamitin da ya gayyaci Ministan harkokin cikin gida, da kuma Kwanturola Janar na Hukumar Kula da gidan gyaran hali na Kasa (NCoS) da Babban Lauyan Gwamnatin tarayya domin su binciki halin da ake ciki a gidajen gyaran hali a fadin kasar nan.
Wannan a cewar ‘yan majalisar na nufin hana sake aukuwar fasa gidajen yari a nan gaba.
Majalisar dattiwan ta bayar da wannan umarni ne ga kwamitin ta bayan da wani dan majalisar tarayya Sanata Istifanus Gyang ya ja hankalin ‘yan majalisar kan harin da aka kai a wani gidan gyara hali da tarbiyya a garin Jos na jihar Plateau a karshen mako da kuma harin da aka kai kan wasu al’ummomi biyu a karamar hukumar Bassa ta jihar.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Sanata Gyang ya ce harin wani koma-baya ne ga zaman lafiya a jihar Plateau ta Arewa inda ya yi kira da a samar da ingantaccen tsarin kula da tsaro domin hana kai hare-hare a gidajen gyaran hali a fadin kasar nan.