By Abbas Yakubu Yaura
Jami’an runduna ta musamman na rundunar ‘yan sandan Najeriya sun kama jimillar mutane talatin da biyu (32)da ake zargi da hannu a laifukan garkuwa da mutane, fashi da makami, safarar makamai, mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, da fataucin miyagun kwayoyi, da Satar motar kan iyaka, fyade, da sauran laifuka.
Rundunar ‘yan sandan ta kuma kwato bindigu guda goma sha tara (19) kirar AK47, da GPMG guda daya (1), da bindigu guda uku (3),da kirar wata bindiga G-3 guda biyu (2) sannan da SMG guda (1), da bindigar berretta guda daya (1) da harsasai guda dari hudu da hamsin da uku (453) masu girman gaske daban-daban,sai karin wasu goma sha biyu (12) da motoci goma sha bakwai (17) da aka kwace daga hannun masu laifin a yayin gudanar da bincike.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Wani abin lura a cikin masu aikata laifukan da aka kama wandanda suka hada wasu mashahuran mutane shida (6) da suke da hannu wajen satar motoci a sassan kasar nan musamman Nasarawa, Fatakwal, birnin taryya Abuja FCT, Kebbi da kuma jihar Zamfara.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Najeriya, CP Frank Mba yace “wadannan wadanda ake zargin suna safarar motocin da aka sace ta kan iyakokinmu na kasa da kasa suna kai irin wannan kayayaki zuwa ga wani babban mai aikata laifuffuka mai suna Alhaji Garuba (har yanzu) a Jamhuriyar Nijar”.
“Bincike ya nuna cewa tsarin da wadanda ake zargin suke amfani da shi ya hada da kwace motocin da karfin bindiga,sannan wani lokaci kuma ana sace motocin ne daga wurin da ake ajiye motoci musamman wuraren shakatawa da gurin bauta kamar Cinema, Coci-coci da Masallatai.
“Ana sayar da wadannan motoci ne a kasashen da ke makwabtaka da Najeriya a kan farashi ba tare da bata lokaci ba, a wasu lokutan kuma a kai wa Alhaji Garuba ayi mu sanya dashi ya bada muggan makamai a madadinsu.
“Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta Interpol tuni ta hada kai da takwarorinsu na jamhuriyar Nijar domin kamo wadanda ake zargi da gudu domin gurfanar dasu a gaban kotu.
“Na biyu kuma shi ne kama wani mai shekaru 27 mai suna Dayyabu Mohammed dan karamar hukumar Soba ta jihar Kaduna bisa laifin mallakar bindigogi kirar AK47 guda biyar (5) da alburusai 250 na AK47 ba bisa ka’ida ba.
Hakazalika jami’an sun kama wasu gungun mutane shida;Mohammed lawali, Suleiman Ibrahim,Mohammed Rebo, Bashir Audu, Monsoru Abubakar da Abubakar Hamidu, dangane da harin da aka kai a wani masallaci da ke unguwar Mazakuka a karamar hukumar Mashegu a jihar Neja inda aka ce mutane goma sha takwas (18) sun mutu sannan an sace sama da mutane talatin (30)
Binciken da rundunar ‘yan sandan ta gudanar ya nuna cewa shugaban ‘yan kungiyar, Mohammed lawali da wasu daga cikin ‘yan kungiyar sun tsere daga gidan yarin Lokoja.
An kama Bashir Audu ne da laifin kai wa ‘yan kungiyar miyagun kwayoyi, an kwato bindigogi biyu (2) kirara AK47, da harsasai guda uku (3) masu rai, da kuma tarin kwayoyi daban-daban.
Good