Jam’iyyar NNPP ta ce yanzu haka tattaunawa tayi nisa tsakanin su da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party Peter Obi.
Peter dai yanzu haka shine ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Kuma shine suke fatan ya zama mataimakin dan takarar su na shugaban kasa wato Rabi’u Musa Kwankwaso.
NNPP ta bayyana hakan ne a yau Asshar, a shafin jam’iyyar ma Twitter, kamar yadda suke fatan kudirin nasu ya tabbata.
Sanarwar ta kara da cewa tuni aka sanya kwamitin mai karfi don kula da batun, kuma shine zai tabbatar da sun samu Peter Onu matsayin mataimakin Kwankwason.
A jiya Juma’a ne dai hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ke cika kan batun mataimakin shugaban kasa ga jam’iyyun siyasar kasar nan.
Yanzu haka dai tuni jam’iyyar PDP ta sanar da gwamnan Delta Eyeanyi Okowa a matsayin mataimakin dan takarar shugaban kasar ta, ita kuma APC ta mika sunan wanda suke fatan ya zama mataimakin dan takarar shugaban kasar su.