Wani jigo a jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Buba Galadima, ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Rabi’u Musa Kwankwaso ne zai gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Ya ce Kwankwaso ne zai lashe dukkan jihohin Arewa maso Yamma da kuma samun isassun kuri’u a sauran yankunan kasar nan a zaben shugaban kasa na shekarar 2023.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamna Ganduje Ya Kafa Kwamitin Da Zai Binciki Jami’ar Jihar
Galadima ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ya yi da Arise TV kan batutuwan da suka shafi siyasar Najeriya.
Ya ce, “Arewa-maso-Yamma na da masu kada kuri’a akalla miliyan 24. Kuma duk wannan fili da ake kira Arewa-maso-Yamma, an bar wa Zaki wato (Kwankwaso) shi kadai.
“Ya kamata ‘yan Najeriya su san abin da yake fuskantar su. A dauki Arewa maso Gabas inda na fito, Kwankwaso zai ci Bauchi, zai ci Gombe, zai ci Adamawa, zai ci Taraba. Jihohin da zai yi kokawa da APC su ne Borno da Yobe.
“Idan ka dauki Arewa ta Tsakiya, za mu ci Filato, za mu ci Nasarawa, a fasahance za mu ci Benue, tabbas Kogi ne gidansa na biyu. Za mu ci Nije, kuma yanzu Kwara daga ziyararmu, ta fada cikin komarmu
“Za mu ci Cross River, za mu ci Akwa Ibom, za mu ci Edo, za mu ci Oyo. Muna fafutukar nemon samun nasara a Delta. Idan Delta ta shigo cikin jihohin da Kwankwaso ya ci a zaben, to babu shakka shi ne zai zama shugaban Najeriya.”
Galadima ya kuma ce ko da an yi siyasar kabilanci a zaben shugaban kasa, Kwankwaso zai yi nasara.
“Kuma idan aka yi siyasar bangaranci, kabilanci da addini, abin da zai faru shi ne Kwankwaso zai zo na daya da kuri’u mafi yawa, kuma kowa zai iya zuwa na biyu, Amma Kwankwaso ne zai zama Shugaban kasan Tarayyar Najeriya,” inji shi