By Ishaq Dabai
Hukumar Tsaro ta Najeriya NSCDC,reshen jihar Kwara ta tabbatar da kisan wani makiyayi da har yanzu ba a san ko su waye ba a jihar.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke dasa hannun Kakakin Rundunar, Mista Babawale Afolabi, kuma aka bai wa manema labarai a Ilorin ranar Juma’a da yamma.
A cewar sanarwar, wannan abin takaici ya faru ne kwanaki kadan bayan da aka samu rahoton mamaye gona a Oro Ago, wanda ake zargin wasu ‘yan bindiga dayi, inda mutum daya ya mutu.
“An kawo rahoton marigayin zuwa ofishinmu ranar Juma’a, ta hannun Jami’inmu Najimu Lawal a Oro Ago,yace harin ya faru ne a ranar 30 ga watan Satumba, yayin da ake zargin wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai farmaki gidan mamallakin shanun inda kuma suka bar shi cikin jini kwance.
Kakakin yace dan uwan marigayin ya rasa ransa a farkon shekarar 2021,a wurin da aka kashe dan uwan nasa.
Afolabi yace an fara farautar wadanda suka aikata laifin.Ya ba da tabbacin cewa NSCDC tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro za su kamo wadanda suka aikata laifin tare da tabbatar da gurfanar da su bayan kammala bincike.