Wata budurwa baƙar fata mai amfani da @diaryofdom__, a TikTok, ta gayawa mutanen kuɗin da ta samu tana aiki a matsayin soja a ƙasar Amurka a shekarar 2022.
A wani ɗan gajeran bidiyo da ta sanya, ta tsara kuɗaɗen da ta samu domin nuna ta yadda suka shigo a kowane wata. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA: Yadda wani ƙaramin yaro ya kitsa sace mahaifin sa, ya karɓi maƙudan kuɗaɗen fansa
A watan Janairu ta samu kuɗi $8,836,59. A wata na gaba mai bin Janairu, shi ma hakan ta samu.
A watannin Maris, Afrilu da Mayu ta samu $8,986.35 (N4,044,306.82), $9,182.19 (N4,132,444.61) da $26,725.44 (N12,027,784.27) (kuɗaɗen alawus).
Sauran sun haɗa da:
WatanYuni ($9,182.19), watan Yuli ($11,458.15), watan Agusta ($9,587.19), watan Satumba ($9,587.19), watan Oktoba ($9,587.19), watan Nuwamba ($9,587.19), da watan Disamba ($9,587.17).
Wani bincike a shafin Payscale ya nuna cewa:
Rundunar sojin Amurka na biyan sojojinta abinda bai gaza $65,352 a shekara. Ƙarancin albashi a rundunar sojin Amurka yana farawa daga $34,460 zuwa $122,608 a shekara.
Ku kalli bidiyon a nan.
Budurwar ta gayawa mutane cewa su je su tabbatar su gani ko ƙarya ta shirga musu.
Bidiyon Budurwa Na Sharɓar Kuka Kan Saurayi Ya Ɗauki Hankula
A wani labarin na daban kuma, wata budurwa ta kama rusa kuka bayan saurayin ta yaci amanarta.
Wata budurwa ta kama rusa kuka bayan saurayinta yayi mata halin samarin zamani.
Wani bidiyo da ya karaɗe manhajar TikTok ya nuna yadda budurwar take ta rusar kuka bayan saurayin na ta yaci amanarta.
Wani mai amfani da @hayourmide_ shine ya sanya bidiyon a manhajar TikTok.