Hukumar lafiya ta duniya ta ce Najeriya ce kasar da ta fi kowacce yawan mace-mace tare da tabbatar da kamuwa da cutar kyandar biri a nahiyar Afirka.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Daraktan yankin na hukuamar WHO a Afirka, Dr Matshidiso Moeti, ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin wani taron manema labarai da aka yi wa lakabi da, ‘Hanyar kawar da cutar kyandar biri nan da shekarar 2030.’
Najeriya, a cewarta, ta samu rabin adadin wadanda suka mutu da ke da alaka da cutar, yayin da wasu aka samu rahoton a Ghana da kuma a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.
“Ga cutar ta kyandar biri, yanzu an tabbatar da bullar cutar guda 524 da kuma mutuwar mutane 12 a cikin kasashen Afirka 11,” Inji “Yawancin lokuta suna cikin Najeriya, DRC da Ghana. Daga cikin 12 da suka mutu, shida sun faru ne a Najeriya, hudu a Ghana, biyu kuma a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.”
Karanta kuma: Gwamnatin Tarayya Ta Ankarar Da Jami’an Lafiya Kan Cutar Kyandar
“Ko da yake ba a bada wata alama ga kamuwa da cutar kyandar biri guda daya ba a kowace cikin kasashen Afirka da ke ba da rahoton bullar cutar, WHO ta ba da na’urorin gwaji 39,000 ga kasashe, wanda ya ba da damar ingantattun adadin gwaji,” in ji Moeti a tweeta.
A halin da ake ciki kuma, binciken da gidan talabijin ta Channels ta yi a ranar Juma’a ya nuna cewa har yanzu Hukumar Yaki da Cututtuka masu yaduwa ta Kasa (NCDC) ba ta sabunta bayanan a shafinta na intanet ba.
Dangane da rahoton yanayi na karshe kan cutar kyandar biri mai kwanan wata 14 ga watan Agusta kuma hukumar NCDC ta buga, Najeriya ta samu mutuwar mutane hudu da ke da alaka da cutar a lokacin.
A cikin rahoton, ta ce an samu rahoton mutuwar mutane hudu a jihohi hudu yayin da jihohi 29 da babban birnin tarayya (FCT) suka bayar da rahoton bullar cutar kyandar biri guda 530 a cikin makonni 32.
“Daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa 14 ga watan Agusta 2022, Najeriya ta samu mutane 530 da ake zargi da kamuwa da cutar tare da 220 da aka tabbatar sun kamu da cutar (maza 144, mata 76) daga jihohi 29 – Legas (35), Ondo (18), Rivers (16), Bayelsa (14), Adamawa (13), Delta (12), Edo (12), FCT (10), Abia (9), Nasarawa (9), Anambra (8), Imo (8), Ogun (bakwai), Plateau (shida), Taraba (biyar), Kwara (biyar), Kano (biyar), Gombe (hudu), Cross River (hudu), Oyo (hudu), Borno (uku), Benue (uku), Katsina (uku), Kogi (biyu) , Niger (daya), Bauchi (daya), Akwa Ibom (daya), Ebonyi (daya) da Osun (daya),” in ji NCDC.
“An samu rahoton mutuwar mutane hudu daga jihohi hudu a shekarar 2022 – Delta guda (daya), sai Legas guda (daya), Ondo kua guda (daya), sai kuma Akwa Ibom da ke da guda (daya).”
A wani labarin kuma: Yara Uku Sun Mutu A Ruftawar Wani Ginin A Jigawa
Yara 3 ne aka rawaito sun mutu sakamakon ruftawar gini biyo bayan samun ruwan sama da aka shafe sa’o’i ana yi a Jigawar Tsada da ke karamar hukumar Dutse a jihar Jigawa.
Wadanda abin ya shafa sun hada da Farida Idi ‘yar shekara shida da Mariya Idi ‘yar shekaru uku da kuma Bilkisu Yahya ‘yar wata 18 da haihuwa duk mazauna kauyen Yakasai Jigawar Tsada.