Shugaban kasa Muhamamdu Buhari ya karbi bakuncin wasu dattawan Katsina a fadar gwamnati a ranar Talata Nan, a Abuja karkashin jagorancin gwamna Rt Hon Aminu Bello Masari kan matsalar rashin tsaro a yankin arewa maso gabas musamman jihar Katsina.
Masari ya jagoranci tawagar jiharsa zuwa wata ganawar sirri da shugaban a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Dattawan sun hada da Sanata Abba Ali (Wanda su kayi aji guda tare da Shugaban Kasa), Alh Aliyu Mohammed, Sanata Mamman A. Danmusa, Alh Nalado Y. Sarkin Sudan da Alh Amhmed Yusuf.
Comments 1