Hukumomin Burtaniya sun kammala yanke shawarar sake duba dokar hana zirga-zirgar da aka sanya wa Najeriya da wasu kasashe 10 a daidai lokacin da aka gano cutar Corona Nau’in Omicron.
Sajid Javid, Sakataren Lafiya na Burtaniya ne ya bayyana hakan yayin da yake yiwa majalisar dokokin Burtaniya bayani a yau Talata.
Ya shaida wa ‘yan majalisar cewa Ingila za ta cire dukkan kasashe 11 daga cikin jerin kasashen masu hadarin yada cutar daga karfe 4:00 agogon GMT a ranar Laraba.
Sakataren Lafiya ya ce dokar Hana wasu kasashe shiga kasar Bai da Wani amfani wajen dakatar da yaduwar sabon cutar Corona Samfarin Omicron.
Ya ce: “Don haka zan iya ba da sanarwar yau cewa yayin da za mu ci gaba da daukar matakan gwaji na wucin gadi don balaguron kasa da kasa, za mu cire dukkan kasashe 11 daga jerin kasashen da muka haramtamawa shiga kasar mu daga karfe 4 na safen gobe.”
idan za’a iya tunawa dai jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito Wasu daga cikin kasashen da Birtaniya ta Haramtawa shiga kasar irin su: Angola, Botswana, Eswatini, Lesotho, Malawi, Mozambique, Namibia, Najeriya, Afirka ta Kudu, Zambia da Zimbabwe.