Rundunar yan sandan jihar Zamfara ta ja hankalin al’umma kan suyi watsi da wani faifan bidiyo dake yawo a kafafen sada zumunta yanzu haka.
Bidiyom dai na bayyana cewa akwai yiwuwa wasu bata gari zai kai hari kan wasu coci a jihar Zamfara.
Sanarwar da mai magana da yawun rundunar SP Mohammed Shehu ya aikowa da Jaridar Dimokuraɗiyya ya bayyana cewa wannan bidiyon da ake yaɗawa tsoho ne domin kuwa an nade shi ne tun a shekarar 2021.
A nasa bangaren Kwamishinan yan sandan jihar Zamfara CP Ayuba N. Elkanah psc. Ya bukaci jama’ar jihar da su ci gaba da kwanciyar da hankalin su domin kuwa rundunar su zata ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen kare lafiyar al’ummar jihar.
Labaran karya dai na daga cikin abubuwan da ke ci gaba da kawo tsaiko ga wasu ɓangarori na ci gaba a Najeriya.
Hakan ya sanya kungiyoyi da hukumomi masu zaman kan su, ke ta kokarin ganin sun fadakar kan illar da labaran karya ke da shi. Cikin al’umma.
Comments 1