Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Kasa NRC ta sanar da dawo da ayyukan layin dogo daga Abuja zuwa Kaduna bayan dakatarwar da aka yi a ranar Juma’a.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Daraktan ayyuka na hukumar, Mista Niyi Alli, a cikin wata sanarwa, ya ce za a fara aiyukan ne a ranar 31 ga watan Janairu.
KARANTA HAKANAN Fasinjoji Sun Makale Yayin Da Jirgin Kasan Kaduna-Abuja Ya Kauce Hanya
“Hukumar Kula da Jiragen Kasa suna farin cikin sanar da sake fara aikin titin jirgin Abuja zuwa Kaduna.
“An dakatar da hidimar ne a ranar 27 ga watan Janairu, saboda lalacewar da ya afku ga jirgin a tashar Kubwa a wannan ranar.
“Daga baya, za a ci gaba da jigilar a ranar 31 ga watan Janairu, tare da jadawalin yau da kullun – KA2 zai tashi daga Rigasa a karfe 07:00; AK1 zai tashi daga Idu da karfe 10.00; KA4 zai tashi daga Rigasa da karfe 13.00; AK3 zai tashi daga Idu da karfe 16.00.
“Duk da haka a ranar Laraba, KA2 kawai zai tashi Rigasa a 0700 kuma AK 3 zai tashi daga Idu da karfe 16.00,” in ji Alli.
Daraktan ya bayyana nadamar duk wani rashin jin daɗi da fasinjojin suka fuskanta sakamakon dakatar da ayyukan na wucin gadi.
Jaridar Daily trust ta rawaito cewa, Sai dai ya bayyana kudirin gwamnatin tarayya na samar da amintattun ayyuka ga jama’a. (NAN)
A Wani Labarin Kuma Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Karar Da Ke Neman A Tsige Buhari
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Litinin din nan ta yi watsi da karar da tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Hope Democratic Party, Cif Ambrose Owuru ya shigar kan zaben shugaban kasa, Muhammadu Buhari a zaben shugaban kasa na 2019.
Mai shari’a Inyang Ekwo ne ya kori karar da ke neman a Buhari kan wasu dalilai guda uku.