Wani ɗan gajeran bidiyon wata kyakkyawar budurwa da mijinta wanda yake wada ne ya karaɗe yanar gizo, inda dubunnan mutane suka kalle shi.
kyakkyawar budurwar mai diri ta sanya bidiyon ne a manhajar TikTok domin nuna yadda ita da mijinta suke rayuwar jindaɗi a matsayin su na ma’aurata.
KU KARANTA KUMA: Wata matar aure ta lakaɗawa mijinta dukan kawo wuƙa saboda yayi mata kishiya
Jaridar Legit.ng ta tattaro cewa budurwar wacce take amfani da sunan @www.kahboh a TikTok, ta haɗa wasu hotuna guda biyu tare waɗanda suka nuna yadda aka ɗauke su a wurare daban-daban.
A ɗaya daga cikin hotunan, mijin nata yana tsaye a gabanta yayin da ta ɗora hannayenta a kafaɗar shi cikin shauƙin ƙauna.
A wani hoton kuma, mutumin yana tsaye a bayanta sannan hannayen sa na kan ƙugunta cikin wani salo na ƙwarewa.
Mutane da dama a TikTok sun yaba da ganin budurwar da mijinta, inda abun yayi matuƙat burge su. Ta dai bayyana cewa su duka biyun suna cikin farin ciki.
Ga kaɗan daga cikin ra’ayoyin da mutane suka bayyana waɗanda Dimokuradiyya ta tattaro:
@onyinyechi ta rubuta:
“Indai har ku duka kuna farin ciki.”
@danilove ya tambaya:
“Wai me ya hanani aure ne?
@Gabriella Tiwaah ta rubuta:
“Ina muku fatan wannan murmushin ya cigaba da kasance a fuskokin ku kada ya taɓa dusashewa.”
@Winnie ta rubuta: ”
“Indai har kuna tare cikin farin ciki.”
@Anita Ivie ta rubuta:
“Wai wannan ƙauna ce. Huhuhuhu.”
@ssemakulafahad4 ya rubuta:
“Yakamata a sanar da mu wannan ƙauna ce ko kuɗi.”
Ku kalli bidiyon a nan
So Baya Da Kama: Hotunan Wasu Masoya Sun Ɗauki Hankula Sosai
A wani labaran na daban kuma, wasu masoya sun ɗauki hankula sosai bayan bayyanar hotunan su a tare.
Bidiyon wani saurayi da budurwar sa wacce ta kasance wada ce ya ɗauki hankula sosai.
Daga sanya bidiyon har sama da mutum duba ɗari uku sun kalla a manhajar TikTok.