Babban Daraktan hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Legas, LASEMA, Dr Olufemi Oke-Osanyintolu, ya bayyana cewa hukumarsa ta yi nasarar ceton wani mutum da ya nemi ya kashe kansa a daidai National Bus Stop, dake Ikeja.
Oke-Osanyintolu ya bayyana hakan ne a yayin ganawarsa da manema labarai a Legas. A cewarsa, mutumin ya nemi halaka kansa ne ta hanyar fadowa da ya yi daga wani gini mai tsayi a ranar Asabar, inda aka buga musu waya aka shaida musu hakan.
Sai dai ya ce hukumarsu ta LASEMA ta yi nasarar cetonsa da ransa. Ya ce bayan samun kiran wayar da suka yi ne suka hanzarta zuwa wurin, inda jami’ansu suka yi nasarar cetonsa, sai dai sun ce ya ji ciwo sosai a kafarsa ta hagu.
Oke-Osanyintolu ya ce mutumin har wala yau ya karye sakamakon neman kashe kansa da ya yi, inda ya ce kuma mutumin yana cikin maye.
Ya zuwa hada wannan rahoton tuni aka mika shi Asibitin Ikeja General Hospital domin ci gaba da yi masa magani. Inda su kuma hukumar suka ci gaba da magani domin gano dalilan da ya sanya yake son kashe kansa.