Wani da ake zargin barawon mota ne mai suna Abubakar Mohammed ya tsallake rijiya da baya daga hannun wasu fusatattun mutane a kasuwar zamani ta Kure Ultra Modern Market da ke Minna babban birnin jihar Neja bisa zargin satar mota kirar Honda Civic.
Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis din da ta gabata yayin da wanda ake zargin dan shekara 40, mazaunin Tudun-Fulani, Bosso, karamar hukumar Bosso, ya yi yunkurin tuka motar, mai lambar Reg No. KAG 371 AA, daga Kasuwar Kure zuwa cikin daji.
Karanta nanZamfara: Kaddarorin Naira Miliyan 273 Sun Lalace a Shekarar 2023 – Hukumar Kashe Gobara
Shaidun gani da ido sun ce bayan kamashi matasa sunyi yunkurin halaka shi amma an kubutar da shi daga fusatattun matasan inda jami’an ‘yan sanda suka tafi dashi.
A yayin da ake yi masa tambayoyi, Abubakar ya amsa cewa ya dauke motar daga wurin ajiye motoci da taimakon wani mabudi wanda ya kirkira.
A cewarsa na shirya kai motar zuwa wurin mai karba na na yau da kullun, wani Bashir Mohammed na yankin Mando a jihar Kaduna.
Wanda ake zargin ya ci gaba da bayyana cewa kafin yanzu, ya saci wata jar mota kirar Honda Civic a kasuwa daya a watan Maris din 2023.
Na sayar da motar ga Bashir guda da ke Kaduna a kan kudi N200,000, wadda na yi amfani da ita wajen sana’ar takalmi a Kasuwa-Wanbai a Jihar Kano.
Na bukaci karin kudi don aikin noma da gina gida a Wushishi domin in shirya wa kaina aure. A halin yanzu, ba ni da mata. Wadannan su ne dalilan yunkurin sake satar mota a kasuwa inji shi.
A wani labarin kuma‘Dalilin Da Yasa Gwamna Mutfwang Ya Ziyarci Tinubu’ – Hadimin Gwamna
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya ce ‘yan sandan sun yi nasarar ceto wanda ake zargin ne biyo bayan kiran da suka yi da lamarin da ya faru a kasuwar.
Ya bayyana cewa a halin yanzu ana kan binciken lamarin a sashin binciken manyan laifuka na jihar, SCID, Minna.
Ya kara da cewa, ana ci gaba da kokarin jami’an rundunar na zuwa jihar Kaduna domin ganin an kama Bashir Mohammed, wanda ake zargi da karbar motocin sata.