Leeds United za ta fara yunkurin dauko dan wasan gaba na Middlesbrough, Chuba Akpom a wannan bazarar.
A cewar TalkSPORT, Leeds ta na da burin kara ƙarfin tawagarta a wannan bazara, ta hanyar dauko Akpom da wasu yan wasan.
KU KARANTA: Zaben Gwamna: INEC Ta Tabbatar Da Halastaccen Dan takarar Jam’iyar PDP A Ogun
Shafin ya kuma yi ikirarin cewa Crystal Palace da Everton suma suna zawarcin dan wasan wanda haifaffen Najeriya ne.
Dan wasan mai shekaru 27 yana jin dadin kakar wasar bana, da tazo mai da ban mamaki tare da kulob din dake fafata gasar Sky Bet Championship, wato Middlesbrough.
Akpom ya zira kwallaye 22 a wasanni 28 da ya buga wa kungiyar da Michael Carrick ke jagoranta a kakar wasa ta bana.
Dan wasan zai sake fafata wasa a gasar firimiya bayan rashin nasarar da yayi a Arsenal.
A wani labarin kuma, Zaben Gwamnoni: Tsohon Gwamnan Sokoto Ya Mika Wata Bukata Ga Al’umma
Wani Sanatan jam’iyyar APC Aliyu Wamakko, ya roki jama’a da su kasance cikin kwanciyar hankali yayin da suka je runfunan zabe domin kada kuri’unsu a zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha da za a yi ranar Asabar. Kamar yadda Daily Post ta ruwiaito.
Wamakko, a wani sako na musamman ga al’ummar jihar Sakkwato, ya ce zaman lafiya shi ne abin da ake bukata na duk wani ci gaba mai ma’ana.