Wata budurwa ƴar Najeriya wacce bata daɗe da haihuwa ba ta bayyana halin da ta tsinci kan ta bayan ta gayawa saurayinta tana da juna biyu.
Ta wallafa wasu hotunan jaririyar ta TikTok da wasu bidiyoyin lokacin da suke tare da mahaifin yarinyar, yayin da take ba jaririyar haƙuri. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Bayan kotu ta yanke hukunci kan aurenta da mijinta, matar aure ta yanke jiki ta faɗi
Ta ba jaririyar haƙuri inda take cewa ta samar mata da uba wanda baya ganin darajar ta.
Budurwar ta kuma wallafa hirar da suka yi da saurayin nata inda ya nuna cewa ba shi bane ya ɗirka mata juna biyu.
A yayin da ta nuna irin son da take yiwa jaririyar, ta bayyana cewa tana fatan cewa watarana zai fahimci irin yadda ɗiyar su take.
Daga cikin hirar ta su, saurayin nata mai suna Chima, tun da farko ya ƙi yarda cewa tana ɗauke da ciki, sannan bayan ya tabbatar tana da cikin sai ya ƙi amincewa na shi ne.
Ya gaya mata cewa ta daina takurawa rayuwar sa. Daga ƙarshe dai ta haƙura ta rungumi ƙaddarar ta, inda take cewa tana fatan nan gaba ba zai zo yace yarinyar tasa ba ce.
Ga bidiyon a nan
Bayan Sun Rabu Da Budurwarsa, Matashi Ya Koma Roƙon Su Cigaba Da Soyayya, Hirar Su Ta Bayyana
A wani labarin na daban kuma, wani matashi ya koma magiya a wajen budurwar da suka rabu kan ta amince su cigaba da soyayya.
Wata budurwa ƴar Najeriya mai suna Darasimi Oyewole ta wallafa hirar da suka yi a WhatsApp da tsohon saurayin ta mai suna Simeon, wanda yake son su dawo su cigaba da soyayya.
Darasimi ta bayyana cewa ya ci mutuncin ta wanda ya kai har sai da ya zazzagi mahaifiyar ta lokacin da ya ƙi sauraron ta.