Dan Wasan Najeriya Kelechi Iheanacho ya sanya hannun kan sabon kwantiragi da zai ajiye shi a Ƙungiyar Leicester City har zuwa shekara ta 2024.
Dan wasan ya zura kwallaye 32 cikin Wasanni 117 da ya buga wa Ƙungiyar yun hadewar sa daga Manchester City a 20017.
A yanzu haka duniyar Kwallo na ci gaba da yi wa Iheanacho dadi bayan da ya zazzaga kwallaye bakwai cikin wasa hudu na baya-bayan nan da ya fafata tare da daukar kyautar Gwarzon dan wasan Firimiya na watan Maris.
Dan wasan ya shaida wa manema labarai cewa abyanzu haka babu inda ya fi mishi Leicester, don zai yi duk mai yiwu na ganin ya cu gaba da samun wuri a Ƙungiyar.
Iheanacho ya wakilci Najeriya a gasannin da dama da suka hada da ta yan kasa da shekara 17 da 20 kana kuma ya fafata wasa talatin wa tawagar Super Eagles kawo yanzu