Gasar tseren motoci ta Fomular 1 gasa ce da ake yinta a sassa daban-daban na duniya. Sai dai za a iya cewa anfi gudanar da ita wannan gasa a can nahiyar turai wadda gasa ce ta tseren motoci da aka saba fafatawa kusan lokaci zuwa lokaci.
Amma kuma a wasan da aka fafata a daren jiya ɗan wasan gasar tseren motoci ya sake kafa wani gagarumin tarihin bayan ya zamo zakara a wasan na tsere da aka gudanar a jiya wato Lewis Hamilton.
Shidai Hamilton ya zamo zakara ne a wasan gasar da aka fafata mai taken Gran Prix a jiya inda ya doke abokan karawarsa dukkansu. Lewis Hamilton ya saba kafa tarihi da dama inda ake ganin a halin yanzu babu gwarzo kamarsa a duniyar tseren motoci ta Fomular 1 wato gasa mai tattare da tarihi.
Lewis dai kowa yasan shahararren ɗan wasan tseren mota ne ya zamo zakara karo na 92 inda babu wani ɗan wasa daya kama ƙafarsa kwata-kwata inda za a iya cewa shine gwarzo a gasar kuma yake da tarihin da bakowane yake da irinsa ba a gasar.
Daga ƙarshe Lewis ya bayyana cewar fatansa shine yaci gaba da samun nasara a dukkanin iya ahekarun da zaiyi a nan gaba yana fafata wannan gasa ta tseren motoci ta Fomular 1 wadda take da farin jini sosai a duniya kuma take ƙayatarwa sosai da sosai.
Suma magoya bayansa daga sassa daban-daban na duniya sun tayashi wannan murna ta zamowa zakara har karo na 92 a daren na jiya. Tabbas za a iya cewa Lewis ya zama gagarabadau a duniyar tseren motici mai taken Fomular 1.