Likitoci ƙarƙashin Ƙungiyar Likitocin Gwamnati da Masu aikin Haƙori NAGMDP, da suke aiki a ƙarƙashin Gwamnatin Jahar Kwara a ranar Litinin, sun fara yajin aikin gargaɗi na kwanaki 7, domin sanyawa a biya masu bukatun su da jindaɗin su.
Shugaban Ƙungiyar Dr. Saka Agboola ya bayyana haka a taron Manema labaru a Ilori, taron shuwagabanni na gaggawa na ƙungiyar da aka gudanar.
Yace Ƙungiyar haƙurin ta ya ƙare, kuma ta daɗe tana bada gargaɗi ga Gwamnatin Jaha akan jindaɗin mambobin ta.

KARANTA WANNAN LABARIN: Jami’an Tsaro sunyi awon gaba da Tsigaggen Kakakin majalisar dokokin Filato
Agboola yace taron Shuwagabannin ya amince da yajin aiki na gargadi na kwanaki 7, inda ya bayyana hakan a matsayin mataki mai ɗaci.
Yace yajin aikin zai bada dama ga Gwamnatin Jahar, dasu a tattauna akan wasu al’amura da suke buƙata, ciki har da samar da yanayi mai kyau, musamman biyan su alawus na mambobin Ƙungiyar.
“Muna da nauye-nauyen iyalan mu, maƙwabtan mu, da kuma marasa lafiya. Akwai buƙatar a baiwa likitoci haƙƙin su domin samun sakamako mai kyau,” inji shi.
A jawabin shi Mr Saad Aluko Darkta-Janar na Hukumar Kula da Asibitoci, yace gwamnatin Jahar na bakin ƙoƙarin ta wajen biyawa Likitocin buƙatun su.
Aluko yace gwamnatin Jahar ta amince da biyan kaso 70 daga cikin 100 na abubuwan da suke buƙata, kuma tuni ta kafa kwamiti dazai samar da matsaya a cikin su.