Rahotannin dake shigo ma Jaridar Dimokuradiyya na nuni da cewa; gwamnatin jihar Kwara za ta bai wa duk wani Likitan da ke aiki wajen yaki da cutar korona alawus na naira dubu 25 a kowacce rana.
AbdulRahman AbdulRasaq, Gwamnan jihar ne ya bayyana hakan a shafinsa na twitter. Inda Gwamnan ya ce sauran ma’aikatan lafiya ma, za su samun alawus daidai da matsayinsu a wurin aikin.
NCDC sun tabbatar da cewa ya zuwa hada wannan rahoto akwai masu cutar korona 16 a jihar ta Kwara.