Wani limamin cocin Katolika a jihar Anambra,Nwaigwe Stephen an gurfanar dashi gaban kotu bisa zargin yi wa wata matashiya fyade da har ta samu ciki, inji rahoton Daily Trust.
Kotun Majistare ta Awka, ta bayar da umarnin tsare Nwaigwe a gidan yari har zuwa ranar 6 ga Disamba, 2023.
Karanta nanAn Kama Mai Damfarar Mutane Akan Rage Farashin Kudin Siminti
Yana cikin wasu limaman cocin da wata kungiyar addini ta kora a garin Orlu na jihar Imo da aka fi sani da Cocin Zuciya Biyu” (Ugwu Nso) a shekarar 2018 bisa zargin rashin da’a.
Alkalin kotun ya umarci mai gabatar da kara da ya mika ainihin fayil din karar zuwa ofishin babban mai shari’a kuma kwamishinan shari’a na jihar Anambra.
A cewar rahoton, an kuma zargi limamin cocin da laifin kai karamar yarinya mai juna biyu da karfin tsiya zuwa birnin Benin na jihar Edo, inda ta haifi jaririnta.
Sai dai binciken da ‘yan sanda suka gudanar ya nuna cewa har yanzu ba a san inda jaririn da aka ce ya ke ba.
Laifin yin jima’i da ƙaramar yarinya yana da hukunci a ƙarƙashin sashe na 34 (2) na dokar kare hakkin yara na jihar Anambra, 2004.
Rahotanni sun bayyana cewa limamin cocin ya gana da matashiyar ne a cocin St. Albert The Great Catholic Church Parish, Obosi, jihar Anambra, inda aka gayyace shi domin gudanar da wani taron cocin.
Yayin da take amsa tambayoyi a gaban kotu a yayin ci gaba da tsare ta a ranar Litinin, 20 ga Nuwamba, 2023, wadda abin ya shafa ta yi ikirarin cewa limamin ya dauke ta daga iyayenta don ta zauna tare da shi tun tana shekara 14, inda ya yi alkawarin daukar nauyin karatun ta yayin da ita ma ta yi hidima a matsayin mai dafa masa abinci.
Ta ce ba da daɗewa ba bayan ta shiga gidan limamin cocin, sai ya fara lalata da ita, inda ta ce ya ci gaba da yin hakan har sai da ta samu juna biyu tana shekara 17.
A wani labarin kumaSojoji Sun Kwato Mutane 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Kebbi
Amma lokacin da na haifi jaririna a gidan wata ma’aikaciyar haihuwa a garin Benin, an gaya mini cewa jaririn ya mutu kuma da na yi kokarin nuna mini jaririn da ya mutu, sai suka ce an binne jaririn.
Mai shari’a Genevieve Osakwe, yayin da take yanke hukunci kan bukatar belin ta bayyana cewa karar da ke gaban kotun laifi ne da ke da hukuncin daurin rai-da-rai, inda ta yi nadamar yadda laifin fyade ga kananan yara ya zama ruwan dare a cikin al’umma.