By Abbas Yakubu Yaura
Mafarauta a unguwar Udawa dake kan babbar hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, sun ceto wasu mutanen kauyen da basu gaza tara ba.
Haka kuma sun cafke wani dan fashi da ke aiki a cikin dajin a kan wannan hanyar.
Idan dai ba’a manta Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa, A kwanakin baya ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan ayarin motocin ‘yan kasuwa dake kan hanyar Kaduna zuwa Kano inda sukayi awon gaba sama da mutane 70 daga cikinsu zuwa cikin dajin.
Sai dai rundunar ‘yan sandan Kaduna, bayan da wasu ‘yan rakiya da suka raka ‘yan kasuwar suka yi nasarar ceto 48 daga cikin ‘yan kasuwar da aka yi garkuwa dasu, yayin da wata ‘yar kasuwa ta bata, kamar yadda jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Mohammad Jalige ya bayyana.
An bayyana cewa mafarautan sun yi wa barayin kwanton bauna ne inda daga bisani suka fada tarkon su.
Wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa mafarauta sun ceto mutane tara da aka yi garkuwa da su.
Ya kara da cewa bayanan, an mika wadanda aka kama zuwa ga hukumomin tsaro.
Amma da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar yace har yanzu rundunar ba ta samu wani rahoto kan lamarin ba.
Sai dai kuma a halin da ake ciki, ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutane biyar a Zariya.
An tattaro cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki Kuregu, a unguwar Wusasa a cikin Zariya inda suka yi awon gaba da mutanen biyar.”Sun zo yankinmu sun yi garkuwa da mutane biyar,” in ji wani mazaunin yankin.