By Ishaq Dabai
Kimanin ‘yan Bindiga 47 ne suka rasa rayukansu bayan da mafaruta suka simamesu a garin Sharoro dake jihar Neja, a cewar PRNajeriya.
A yayin da mafarautan suke gudanar da sintiri a bakin kogin garin Magami zuwa Sharoro da kuma karamar hukumar Rafi suka kashe ‘yan bindigar a ranar laraba.
Wata majiya ta shai dawa PRNajeriya cewa al’ummar dake zaune a kusa da kogin yan bindigar suna amfani da wajen dan su boye tare da kuma kafa sansaninsu.
Rundunar ‘yan sanda ta musamman wadanda suka ce basu da tabbacin adadin yan bindigar da aka harbe akusa da wajen.
“Ina mai fadama muku cewa an samu gawar wasu ‘yan bindigar a cikin ruwa, mafi karancin wadanda aka kashe sun kai 47 a cewa mafarautan.
PRNajeriya tace bata da tabbacin adadin mafarauta nawane suka gudanar da simamen tare hadin guywa ‘yan kungiyar vigilante NSVC wadda aka samar dan su taimakawa jami’an ‘yan sanda wanda gwamnan jihar ya samar dan kula da tsaron jihar.
Yayin kaddamar da kunguyar awatan june na shekarar 2021,gwamna Abubakar Sani Bello yace ayyukan ‘yan bindiga yana cin zarafin mutane da gwamnati wanda hakan bai kamata ‘yan bindigar su canza tsari ba na sajewa acikin mutane.
Sani Bello ya kara da cewa “sai anyi amfani da karfi wajen canza musu rayuwa a jihar naija.
Kazalika ya kara da cewa “sun hana yaranmu zuwa makaranta, sun hana mutane tafiye tafiye, sun hana mutane zuwa gona dan yin noma, amma sai gashi yanzu suna so su dakatar da komai, bazamu laminci wannan cin zarafin ba, bazasu hanamu samun farin cikiba, zamu ciga da rayuwar cikin walwala.