Wani magidanci ɗan Najeriya ya tafi ya bar matar sa a asibiti saboda ta ƙara haiho masa jaririya yayin da shi kuma yake son jariri namiji.
Wata ma’aikaciyar jinya da unguwar zoma a jihar Legas, mai suna Kaykay, itace ta bayyana hakan a manjahar TikTok a ranar Juma’a 31 ga watan Maris 2023. Shafin Yabaleftonline ya rahoto.
KU KARANTA KUMA: PDP Ta Yi Allah-Wadai Kan Kame Da Tsare Mambobinta A Jihar Kebbi
Ma’aikaciyar jinyar wacce taji haushi matuƙa kan abinda magidancin yayi, ta bayyana cewa ta kasa gane meyasa namiji zai ɗora alhaki kan matarsa domin ta haifi ƴaƴa mata ba duka a cikin wannan zamanin da muke ciki yanzu.
A kalamanta:
“Na kasa yarda cewana wannan zamanin da muke ciki yanzu wasu magidanta ƴan Najeriya basu san cewa samun duka ƴaƴa mata ba laifin matar bane..”
“Haka wannan magidancin ya ƙi zuwa ya ga matar sa a asibiti tun bayan da ta haihu kwana uku da suka wuce saboda ta ƙara haiho mace.”
Wasu magidantan dai sun fi sha’awar samun ƴaƴa maza inda ran su bai cika so ba idan aka haifa musu ƴaƴa mata.
Budurwar Cristiano Ronaldo Ta Bayyana Wani Sirri Dangane Da Rayuwarsu Ita Da Dan Wasan
A wani labarin na daban kuma, budurwar Cristiano Ronaldo ta bayyana wani muhimmin sirri game da ita da ɗan wasan
Georgina Rodriguez, budurwar shahararren ɗan wasan ƙwallon kafan nan, Cristiano Ronaldo ta bayyana wani sirri na rayuwar su ita da ɗan wasan.
A cikin jerin shirin fim ɗin ta a Netflix mai suna Georgina, wacce tun shekarar 2016 suke soyayya tare da ɗan wasan, ta bayyana wajen da ba a taɓa zato inda suka mori juna ita da ɗan wasan.