- Wata mata ‘yar Najeriya ta bayyana kaɗuwarta game da jerin sakonni masu ratsa zuciya da mahaifiyarta ta aika a WhatsApp
- Ta tafi yin karatun shari’a a Burtaniya amma a maimakon haka ta yanke shawarar shiga kasuwancin kayan abinci da kafa kantin sayar da kayayyaki na Afirka
- Mahaifiyarta ta ki amincewa da sana’ar ɗiyartata, inda ta ce abin kunya ne ga wanda zai karatun lauya ya yi hakan, ta kuma sha alwashin hana ta.
Wata mata ‘yar Najeriya ta yi barazanar kin amincewa da ‘yarta saboda ta shiga harkar sayar da abinci a kasar Burtaniya.
Budurwar, mai suna Chioma Brown, ta bayyana barazanar mahaifiyarta ta kafar sadarwar TikTok yayin da ta bayyana rashin jin dadin ta game da wannan ci gaba mai ratsa zuciya.
A wasu saƙonni da aka tura cikin dandalin WhatsApp ya nuna yadda mahaifiyar tace Chioma ta bata mamaki ganin cewar ƙannanta na nan gida sunyi aure suna ta haihuwa abinsu ita kuma tana can tana siyar da kayan miya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wani matashi ya yi bikin taya kakan-kakansa murnar cika shekaru dari da casa’in 190 a raye.
Mahaifyar wacce ta ce kasuwancin da Chiman take kasaƙanci ne a wajenta, ta yaya zata kalli ‘yan uwanta ta ce musu Chioma da ta tafi karantun Lauya a ƙasar Turai ta koma siyar da kayan miya.
Ta ƙara da cewa matuƙar ta cigaba da sai da kayan miyan to tabbas ta sallamata a matsayin ‘yarta.
Da yawa daga cikin masu amfani da shafin sada zumuntar sun bayyan ra’ayoyinsu kamaer haka:
@4715802164446 yace: “Ya kamata kiyi ƙoƙari ku sulhunta ta bayan fage. Yanar gizo bata manta abu kuma nan gaba kaɗan zaki da kin sani. Ki kula da kanki:
@Cypha_micro tace: ” Duba da abubuwan dake ƙasa, da alama kasuwancin da take tafi samun nasara akansa. Kada ki yi fishi, kalamanta ne kawai suke ƙona miki rai, amma tabbas za kiyi nasara.
@Kinoni86 yace: “Ke fa ba yarinya bace, kiyi kawai abinda zai faranta miki rai”
@Tenderness tace: “Tana ta faɗin me zata gayawa ƙawayenta, hakan na nufin ba ta’yartata take ta ba ta ƙawayenta take”