– Kakansa ya cika shekaru 190 a duniya, ya taya shi murna.
– Matar kakannasa ita kuma shekarunta 163 a duniya.
– Wasu na yi masa fatan ƙara shekaru 50 a nan gaba.
Wani matashi ya yi bikin taya kakan-kakansa murnar cika shekaru dari da casa’in 190 a raye.
Matashin ya rubuta cewar: “Wannan shine kakan-kakana wanda ya cika shekaru 190 a raye.”
Ya kuma kara da cewar “Baya iya magana sannan ya samu shafewar ƙwaƙwalwa, kawai muna dan fito da shi waje ne domin ya ɗan sha iska, amma duk da haka abin alfaharinmu ne mu da muke ‘ya’yan jikoki a wajensa da har yanzu muka tare da shi har ma da matarshi wacce a yanzu haka ita kuma ke da shekaru ɗari da sittin da uku 163 a duniya”
KARANTA WANNAN LABARIN: An yi sunan ‘ya’yan maguna biyu da aka haifa a garin Kano.
“Addu’ar dukkanin iyaye shine su yi nisan kwanan da zasu ga ‘ya’yan ‘ya’yansu sun zama wasu a nan gaba.”
” Kakan-kakana dai ya kasance daya daga cikin waɗan da Allah ya tsawaita rayuwarsu suka sami wannan dammar.” Ya ce.
Jaridar Global Times Nigeria ce ta wallafa wannan rahoton wanda yaja hankalin dayawa daga cikin masu bibiyar kafafen yaɗa labarai daban daban.
Ga wasu daga cikin ra’ayoyin da muka tattaro muku akan wannan rahoton:
@Bernadette Ikolo yace: Allah mai iko… Ina taya kaka murnar ranar haihuwarsa.
@Rowland Effiom yace: Ina fatan kakannan naka ya ƙara shekaru hamsin 50 a nan gaba.
@Emmanuel Anyanwu yace: wannan ai kwata-kwata baya jindaɗin rayuwarsa, kawai ya mutu ya huta shi yafi masa.
Wata mata ta yi raga-taga da motar Mijinta.
A WANI LABARIN: Wata mata ta lalata motar Mijinta ta hanyar farfasa masa gilasan motar.
Matar wacce wani fefen bidiyo da Jaridar Solacebase ta wallafa a shafin ta na Facebook, ya nuna yadda matar ta farfasa gilasan motar mijin nata.
A lokacin da take wannan ɗanyan aikin, bidiyan ya jiyo matar tana shaidawa mijin nata cewar ita ce take lalata masa motar ba wani ba.
Da alama shi kansa mijin yana daga sama yana kallon ɗanyen aikin da matar tasa take yi masa.
A duk fasa gilas ɗaya sai ta ɗaga hannu ta nuna shi sannan ta magantu.
Sai dai bai ce komai ba, ya ja bakinsa yayi shuru inda sauran jama’ar dake gurun suka ta kallanta suna mamakin abinda yasa take wannan ragar-gazar motar mijin nata haka.