Wata uwar amarya ta fashe da kuka a dai dai lokacin da za a tafi kai ‘yarta gidan mijinta.
Uwar amaryar wacce aka hango ta ta rungume’ ƴar tata a wani yanayi na bankwana da ƴar domin tafiya ibadar aure.
Hakan dai ya faru ne a wani fefen bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta na zamani daban daban.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wani Jarumin Maza kuma Zaƙaƙurin Ango Zai Angwance Da Mata Huɗu Rigis A Rana Ɗaya
Tun da farko dai ‘yarce tazo wajen mahaifiyar domin yiwa mahaifiyarta sallama da kuma neman a saka mata albarka a tafiyar ibadar da zata yi.
Mahaifiyar tayi kokarin riƙe kanta kar ta yi hawaye a gaban ƴartata amma hakan yaci tura.
Bayan da ta gama rungume yar ne, sai kawai aka hango ta ta ɗauki gefen mayafinta ta rufe fuskarta tana kuka har na tsawon wasu loƙuta.
Ita ma ƴar an hango ta tana nata kukan rabuwa da mahaifiyar tata a dai dai lokacin da ƴaruwarta ta rike hannunta domin tafiya da ita.
KALLI BIDIYAN
Ita kanta ƴar uwar amaryar an hango yanayin nata ya canza tana shirin zubar da nata hawayen.
Bidiyan ya samu makallata da dama inda wasu da yawa suka tofa albarkacin bakin su akai.
A WANI LABARIN KUMA: Da Alama Karamar magana na shirin zama Babba tsakanin Jaruma Sara Alesious wadda aka fi sani da Stephanie da Nasir na cikin shirin Daɗin Kowa
Jaruman fim ɗin nan mai dogon zango mai suna Daɗin Kowa wanda tashar talabijin ɗin Arewa 24 take haskawa a duk mako, wato Stephanie da Nasir na shirin angwancewa.
Tashar Arewa 24 ce dai ta wallafa hotunan nasu samfurin ‘pre wedding pictures’ aka kuma rubuta ‘Kar ku bari a baku labari’ a kasan hotunan.
Bayan waɗan nan hotunan tashar talabijin ɗin ta saka wani bidiyo wanda shima dai yake ɗauke da hotunan Nasir da Stephanie.
Tun farko dai Nasir da Stephanie sun kasance ma’aurata a cikin shirin ‘Daɗin Kowa’ wanda Tashar ta Arewa TV take haskawa.