By Abbas Yakubu Yaura
Allah ya yi wa Hajiya Murja Bara’u, mahaifiyar Alhaji Dahiru Mangal, mai kamfanin Max Air, rasuwa.
Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Katsina a majalisar dokokin jihar, Hon.Ali Abu Albaba,ne ya tabbatar da hakan a safiyar yau.
Majiyoyi sun ce ta rasu ne a daren jiya bayan gajeriyar jinya tana da shekaru 85 a duniya.
Ana sa ran za’ayi Sallar Jana’izarta a Masallacin Mangal dake Kofar Kwaya, bayan Sallar Juma’a.
Sai dai wasu majiyoyi sun ce za a yi sallar jana’izar ne a gidanta da ke Kerau a cikin birnin Katsina da karfe uku na rana.