Wani mutum dan shekara 62 a jihar Adamawa ya yi wa wata yarinya ‘yar shekara 14 fyade da aka bashi amanarta.
Jaridar DAILY POST ta rawaito cewa mutumin mai suna Godwin Sanda, mai sana’ar sayar da maganin gargajiya, ya yi amfani da yarinyar, mai tabin hankali da aka kawo masa domin ya yi magani, a cewar ‘yan sanda.
Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta rabawa manema labarai a ranar Lahadin, inda ta ce jami’anta sun kama wanda ake zargin a ranar Asabar, 23 ga watan Yuli, bisa laifin aikata laifin fyade.
“Wanda ake zargin, Godwin Sanda, mazaunin kauyen Zagun, cikin karamar hukumar Numan, ya yi amfani da matsayinsa na mai bada maganin gargajiya don yowa yarinyar fyade da sunan neman magani,” in ji sanarwar.
Sanarwar mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda Suleiman Nguroje, ta ce mahaifiyar yarinyar, Maryam Abubakar ta kai rahoton faruwar lamarin ga hedikwatar ‘yan sanda da ke Numan.
“Bincike na farko ya nuna cewa wacce aka lamarin ya shafa tana fama da tabin hankali kuma mahaifiyarta ta garzaya da yarinyar ne wajan wanda zargin domin neman magani.
“A cikin wani yanayi na daban, wanda ake zargin ya shawarci mahaifiyar da ta koma gida har zuwa lokacin da wanda aka kawo zata warke, kuma sakamakon rashin mahaifiyar na tsawon kwanaki biyar ne wanda ake zargin ya samu yin lalata da yarinyar ba bisa ka’ida ba.,” ‘yan sandan sun bayyana.
Rundunar ‘yan sandan ta kara da cewa jami’an ‘yan sanda na CID na gudanar da bincike kan wanda ake zargin bisa ga umarnin kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Sikiru. Akande