Mai ɗakin Gwamnan Kano, Farfesa Hafsah Abdullahi Umar Ganduje ta bayyana cewa gwamnatin Kano za ta ci gaba da kokarin sauke nauyin alkawuran da suka dauka yayin yakin neman zabe.
Farfesa Ganduje ta bayyanawa taron raba tallafi ga mata da matasa a karamar hukumar Kabo cewa ta haka ne kawai za su rage nauyin da ya rataya a wuyan su.
Ta ce tun bayan samun nasara a zaben da ya dawo da su kujerar mulkin jihar ne Gwamna Ganduje ya umarci shugabannin ƙananan hukumomi da su samar da ayyukan raya mutanen dake karkara.
Cikin kayan tallafin da aka raba akwai motoci, da babura, da kuma kudade da sauran kayan tallafi ga wadanda suka koyi sana’o’i.
Wasu daga wadanda suka koyi sana’o’in sun bayyanawa Jaridar Dimokuradiyya cewa suna fatan abin da zasu samu zai taimaka wajen tsayawa da ƙafafuwan su.
Sun kara da cewa mata da dama na shiga wani yanayi a karkara sakamakon rashin abin hannu.
Mutanen karkara kan fuskanci kalubalen rayuwa kama daga rashin kayan more rayuwa kamar hanyoyi da ruwan sha duk da irin rawar da suke takawa a zabukan kasar nan.