By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta kaddamar da wani bincike kan mutuwar wani basarake na Abuja, wanda ake zargin ya rasa ransa a wani otal tare da wasu mutane hudu.
Marigayin Sa’adu Abubakar, jami’in hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (NSCDC), dan shugaban Pai dake karkashin karamar hukumar Gwagwalada a babban birnin tarayya Abuja, amma yanzu yana zaune a Suleja ta jihar Neja tare da iyalansa.
An kama wani shugaban Unguwa a Suleja da wasu ‘yan mata uku da aka ce suna tare da shi a lokacin mutuwarsa.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa a ranar Lahadin data gabata ta rawaito cewa, an yi jana’izar marigayin ne a ranar Juma’a bayan da wasu dattawa suka shiga tsakani don ganin an ceto gawarsa daga hannun ‘yan sanda.
Kokarin tattaunawa da jami’in ‘yan sandan (DPO) reshen ‘yan sandan Suleja, SP Mutala Mustapha, inda ake gudanar da shari’ar bai yi nasara ba.
Bai dauki ko mayar da kiran wayar da wakilinmu ya yi masa ba.