Majalisar Dattawa ta bayyana kudirinta na samar da tsaftataccen ruwan sha ga ‘yan Najeriya
Shugaban Kwamitin Majalisar Dattijan mai kula da albarkatun ruwa Abdulaziz Yari ya bayyana ƙudirin Majalisar ta 10 na yin doka tare da gudanar da ayyukan sa ido kan ayyukan ruwa a faɗin ƙasar nan domin tabbatar da tsaftataccen ruwan sha ga ‘yan Najeriya.
Ya yi magana ne a taron ƙaddamar da kwamitinsa a ranar Alhamis inda ya ce Majalisar zartaswa da sauran masu ruwa da tsaki za su haɗa kai don samar da ruwa mai tsafta daidai da ƙudirin Majalisar Ɗinkin Duniya mai ɗorewa (SDG) mai lamba shida.
Yari mai wakiltar mazabar Zamfara ta Yamma ya ce Kwamitin ƙarƙashin Jagorancinsa zai baiwa Gwamnatin Tarayya tallafin da ya dace domin ganin an samar da ruwan sha mai tsafta da tsaftar muhalli ga ‘yan Najeriya.
Muna sane da cewa ruwa rayuwa ce kuma hakki ne da ya rataya a wuyan Gwamnati ta samar da tsaftataccen ruwan sha ga ɗaukacin al’ummarmu.
KARANTA WANNAN LABARIN:Wani Ɗan daba da ake zargi Ya Miƙa Kansa Ga Rundunar ‘Yan Sanda A Kano
Haka kuma haƙƙi ne da ya rataya a wuyan Gwamnati ta tabbatar da cewa mun yi amfani da dimbin ƙarfin ruwa wajen samar da makamashi don noma da sufuri.
Wannan kwamitin mai kula da albarkatun ruwa zai yi aiki kafada da kafada da ɓangaren zartaswa na Gwamnatin Tarayya na ƙasarmu domin ganin mun taka rawar gani wajen samar da ingantaccen yanayi ga ma’aikatu da hukumomin da suka shafi ruwa.
Mafi mahimmanci za mu yi aiki don ganin cewa aikin wannan kwamiti ya yi daidai da ajandar Majalisar dattawa ta 10, “in ji shi.
Da yake amsa tambayoyi kan wasu kudurori da ake ta cece-kuce a kan zaman da suka gabata daga ‘yan Jarida bayan ƙaddamarwar, Yari ya ce “Wannan ita ce dimokuradiyya ko mene ne manufarmu sai mu saurari bukatun al’ummarmu dangane da kudirorin da muka gabatar da kuma ayyukan da muke so muyi.
Wata kungiya mai zaman kanta ta Wateraid ta bayyana cewa sama da ‘yan Najeriya Miliyan 60 ba sa samun ruwan sha mai tsafta.