Wani Ɗan daba da ake zargi Ya Miƙa Kansa Ga Rundunar ‘Yan Sanda A Kano
Wani Ɗan daba da rundunar ‘yan Sandan Jihar Kano ta bayyana cewa tana nema ruwa a jallo a watan Agustan 2023 ya miƙa kansa ga rundunar tare da wasu ‘yan daba 40.
Idan za ku tuna cewa rundunar ta bayyana Abba Barakita na Dorayi Quarters Nasir Abdullahi wanda aka fi sani da Chile Maidoki na Layin Falwaya Kurna Makabarta Quarters da Hantar Daba na Kwanar Disu da kuma Nasir Abdullahi tuni sun miƙa kansa ga rundunar.
Sai dai ɗaya daga cikin ‘yan daba uku da aka bayyana ana nema ruwa a jallo, Abba Barakita a ranar Alhamis ya mika wuya ga hukumar tare da bayyana tubarsa daga ayyukan ‘yan daba da ake zarginsa da aikatawa.
A cewar Jami’in hulɗa da Jama’a na Rundunar ‘yan Sandan Jihar (PPRO) SP Abdullahi Haruna Kiyawa, tuban ba wai kawai ya mika kansa ba ne, ya kuma shawo kan abokansa guda 40 da su mika wuya, ya kuma ƙara da cewa tubabbun ‘yan barandan sun kuma mika makamansu.
KARANTA WANNAN LABARIN:Shugaban Majalisar Dattawa Akpabio Ya Taya Tinubu Murna Kan Hukuncin Kotun Koli
Ya bayyana cewa bisa la’akari da wannan ci gaba kwamishinan ‘yan sandan Jihar CP Mohammed Usaini Gumel ya bayar da umarnin a riƙa bayyana sunayen ɓarayin da suka tuba da kuma gyara su yadda ya kamata.
A Wani labarin dauka:Tinubu Shugaban Najeriya Ne, Ba ga APC Kadai Ba – Wike
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, a ranar Alhamis, ya bayyana cewa shugaba Bola Tinubu ba wai shugaban jam’iyyar APC ne kadai ba, shugaban Najeriya ne.
Tsohon Gwamnan Jihar Ribas ya bayyana hakan ne a lokacin da jiga-jigan jam’iyyar APC na jihar sa karkashin jagorancin mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa reshen Kudu maso Kudu, Mista Victor Giadom, suka kai masa ziyara a Abuja.
Sai dai ya ce shugaban kasar na da damar daukar muradun jam’iyyar sa a zuciyarsa yayin da yake tafiyar da al’amuran kasar.
Ya ce jam’iyyun siyasa ababen hawa ne da ke isar da mutum zuwa inda ake so, ya kara da cewa muradun ‘yan Nijeriya ya wuce duk wasu bukatu da ke cikin tunanin Shugaba Tinubu.