By Ishaq Dabai
Biyo bayan kudirin da sanata mai wakiltan gundumar Cross River ta kudu, Gershom Bassey, na majalisar dattijai yayi ya bukaci gwamnatin tarayya data gaggauta ayyana dokar ta baci a kan dukkan hanyoyin Gwamnatin tarayya na kasar nan.
A cikin sanarwar da Bassey ya sanya wa hannu da kansa kuma ya bawa manema labarai a Calaba ranar Juma’a, Shugaban Kungiyar Kuros Riba a Majalisar Tarayya yace manyan hanyoyin tarayya a Najeriya na bukatar kudi kimanin Naira biliyan 215 a kowace shekara don sake gyaran kilomita 3,500 na hanyoyin tarayya daga shekara 8 zuwa 10 domin samun cikakken gyaran hanyar.
Bassey ya gabatar da kudirin, mai taken: “kudurin gyara munan hanyoyin da kungiyar ma’aikatan man fetur da Gas takasa (NUPENG) da kuma Kashedin ta fiya yajin aiki” a zauren majalisar dattijai kuma an amince da hakan yana rokon gwamnatin tarayya data yi abubuwan da ake bukata.
Yace daga shekarar 2016-2020, ainihin kudaden da gwamnatin tarayya ta sakarwa FERMA don gyaran hanya kusan kashi 17 cikin dari ne na kudaden da ake bukata kuma wannan ya yi kadan idan aka yi la’akari da irin matsalolin da ake fuskanta a kasa.
Dangane da haka, Majalisar Dattawa a cikin kudurinta ta bukaci Ma’aikatar Kudi ta Tarayya data hanzarta yin wani abu mai matukar muhimmanci na kasa ta saki isassun kudade ga Hukumar Kula da Titin gwamnatinTarayyar don gaggauta gudanar da gyaran cikin gaggawa a kan dukkan hanyoyin tarayya a fadin kasar nan.
Duk da cewa kungiyar NUPENG ta dakatar da yajin aikin na dan lokaci, dan majalisar yace, ma’aikatan NUPENG sun yi barazanar gurgunta tattalin arzikin Najeriya ta hanyar yajin aiki na kasa baki daya idan ba a gyara hanyoyin marasa kyau da kunya ba.