By Ishaq Dabai
Mazauna yankunan jihohin Sakkwato da Neja da abin ya shafa sakamakon rufe hanyoyin sadarwa da gwamnatoci suka sanya don yakar ‘yan fashi da makami sun ce matakin na tsaro ya same su.
Mazauna wasu daga cikin ƙauyukan dake cikin mawuyacin hali sun koka da cewa hare -haren sun tsananta tun lokacin da aka toshe hanyar sadarwar wayar hannu, suna masu cewa ba za su iya yin kiran gaggawa ba ko karɓar kiran gargadi don gujewa hare -haren dake tafe, in ji kamfanin dillacin labarai na AP, An sanya takunkumin sadarwa a ranar 3 ga watan Satumba a jihar Zamfara na farkon makonni biyu wanda daga baya aka kara tsawaita wa’adin, Kodayake an dawo da hanyar sadarwa na wayar hannu a Gusau, babban birnin jihar Zamfara, har yanzu yankunan karkara suna cigaba da zama babu hanyar sadarwa tana yanke.
Jihohin Katsina, Sakkwato, Neja da Kaduna su ma sun takaita hanyoyin sadarwar wayar salula a wuraren da ake ci gaba da kashe -kashe da sace -sace.Yayin da rufewa da farmakin sojoji ya rage ayyukan ‘yan ta’adda, wasu mazauna jihohin sun ba da rahoton munanan hare -hare sakamakon bazuwar yan bindigar.
Fiye da mutane 100 aka kashe a fadin arewa maso yamma da tsakiyar Najeriya a cikin makwanni biyu da suka gabata, a cewar majalisar kan hulda da kasashen waje yayin da wasu da dama ba a ba da rahotonsu ba.”Mun zanta da,” wata ‘yar majalisa a Majalisar dokokin Sokoto, Amina Al-Mustapha, daga Sabon Birni, daya daga cikin wuraren da lamarin ya fi kamari, inda ta shaida mana.
Kazalika Akalla mutane 32 aka kashe a yankin Munya dake jihar Neja a farkon wannan watan lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan kauyuka suka yi musu dirar mikiya na tsawon sa’o’i ba tare da takura su ba saboda babu wani taimako ga mutanen yankin.Mazauna ƙauyen ba su iya aikawa da sakon neman agajiba game da hare -haren, saboda toshe hanyoyin sadarwa, shugaban Munya, Garba Mohammed, yace ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro sun samu labarin hare -haren ne sa’o’i bayan kisan mutanen.
Baya ga toshe hanyoyin sadarwa na jihohin arewa sun kuma rufe kasuwanni, sun kafa dokar hana fitar dare, rage zirga -zirgar ababen hawa, rufe manyan hanyoyi da hana babura hawa domin dawo da tsarin doka.