By Abbas Yakubu Yaura
Majalisar dokokin jihar Kano tace ana shirye-shiryen zartar da dokar kare hakkin yara saboda yadda ta himmatu wajen bunkasa yara da ci gaban jihar.
Shugaban masu rinjaye na majalisar Labaran Abdul Madari ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano.
Yace kudurin dokar ya tsallake karatu na biyu kuma kwamitin majalisar mai kula da harkokin mata zai hada kan malaman addinin musulunci da sauran masu ruwa da tsaki domin a samar da kudirin doka da zai nuna al’adun al’ummar jihar.
Dan majalisar yace majalisar ta zartar da kudirori 19 da kuma kudiri 117 a shekarar 2021.
Sannan ya lissafa kudurorin sun hada da kudirin kasafin kudi na jihar Kano, daftarin kasafin kudi na al’ummar jihar Kano, da dokar kula da basussuka ta jihar Kano da kuma kudirin kula da asusun majalisar.
Ya kara da cewa, “majalissar tana nazarin kudurori 14, wasu anyi musu karatu na biyu yayin da wasu kuma suna tare da kwamitocin majalisar daban-daban.”
Dan majalisar yace nasarar da aka samu ya ta’allaka ne kan kyakkyawar alakar aiki a tsakanin takwarorinsa kuma ya ba da tabbacin za su ci gaba da jajircewa wajen kyautata rayuwar jama’a.