Majalisar dokokin Kano ta tsayar da ranar da zata tantance sabbin kwamishinonin da gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya aike mata.
Yayin zaman majalisar na Litinin din nan, wanda yake gudana bisa jagorancin shugabanta Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari, zauren ya tsayar da ranar Litinin mai zuwa wato 22 ga watan Agusta, 2022 domin tantance su.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Gwamantin Kano ta aike da sunayen sabbin kwamishinonin kuma ‘yan majalisar zastaswar ne domin maye gurbin wadanda suka ajiye aiki don yin takara a matakai daban daban, a zaben 2023 dake tafe.
Shugaban majalisar Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari, ne ya karanta sunayen sabbin kwamishinonin da suka haɗar da Garba Yusuf Abubakar, tsohon kwamishinan kudi zamanin gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau da Lamin Sani Zawiyya da Ibrahim Dan Azumi Gwarzo da Abdulhamid Abdullahi Liman da kuma Ya’u Abdullahi ‘Yan Shana.
Sauran sune Yusif Jibril Rurum da Adamu Abdu Fanda da Saleh Kausani.
Majalisar ta kuma gayyaci mutanen takwas domin tantance su a ranar Litinin 22 ga watan da muke ciki na Agusta.