By Abbas Yakubu Yaura
Majalisar dokokin jihar Ogun ta fara gudanar da bincike kan zargin karkatar da kudade da tsohon shugaban rusasshiyar karamar hukumar Sagamu ta Kudu (LCDA) yayi Barista Hassan Olugbenga.
Majalisar ta hannun kwamitinta mai kula da asusun gwamnati da yaki da cin hanci da rashawa, ta gayyaci tsohon shugaban karamar hukumar da ya gurfana a gabanta a ranar Alhamis, domin bayyana irin rawar da ya taka a kan badakalar kudaden da ake zargin ya aikata a lokacin da yake rike da mukamin Karamar Hukumar.
Kwamitin dai ya bayyana hakan a cikin tambayoyin tantancewa a gaban ‘yan majalisar.
Majalisar ta kuma gayyaci dukkan jami’an kansilolin da ke da hannu a cikin wasu zarge-zargen tafka magudin kudi da aka lura da su wajen nazarin rahoton tantance ma’aikatun kananan hukumomin jihar.
‘Yan majalisar sun fitar da sammacin ne ta hannun babban sakataren dindindin na hukumar yi wa kananan hukumomi hidima.