Majalisar Dokokin Jahar Sokoto a ranar Talata ta amince da buƙatar Gwamnan Jahar Aminu Tambuwal daya ciyowa Jahar bashin biliyan 28.7.
Kamfanin Dillancin Labaru na Ƙasa ya ruwaito cewar, amincewar ta biyo bayan yin dubi akan wasu takardu guda biyu da Gwamnan ya turowa Kwamitin Majalisar kamar yadda Bello Ambarura ya buƙata.
NANNAN ta kuma ruwaito cewar, buƙatar ciwo bashin ta ƙunshi Naira biliyan 18.7 na tallafin Gwamnatin Tarayya, da kuma Naira biliyan 10 a madadin ƙananan hukumomi 23 na Jahar.

KARANTA WANNAN LABARIN: Kaduna: An Bankawa wani Mai Baiwa Yan bindiga Bayanan Sirri Wuta
Ambarura yace bada tallafin Gwamnatin Tarayya na daga cikin biliyan 656.1 da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya taɓa amincewa Jahohi 36 na Ƙasar.
Yace “kuɗaɗen nada manufar tallafawa Jahohi domin su magance matsalolin da jahohi zasu fuskanta wajen biyan basussukan da Gwamnatin Tarayya ta basu na cike giɓin kasafin kuɗi.
Ƴan Majalisar sun ƙara dacewa, za’a yi amfani da kuɗaɗen wajen biyan wasu ayyukan raya ƙasa, da wasu kayayyaki domin cigaban tattalin arzikin ƙasa.
Mataimakin Shugaban Majalisar Abubakar Magaji wanda ya jagoranci zaman majalisar, ya bayyana amincewar Majalisar bayan taron sirri da suka gudanar tare da kwamitin majalisar.