Majalisar dokokin jihar Zamfara ta kaɗa kuri’ar yake kauna ga mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Babagana Mungonu, kan gazawarsa game da matsalar tsaron da ke faruwa a jihar.
Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na majalisar Mustapha Jafaru Kaura, Majalisar da ta yi zamanta a jiya, ta nemi gwamnatin jihar ta kafa wani kwamiti da zai gudanar da bincike kan mutanen da ke dakile kokarin tattaunawar zaman lafiyar da ake yi a jihar.,
Wannan dai wani martani ne da majalisar jihar ke yi game da ayyana jihar a matsayi wadda aka haramta shawagin jirage a samaniyarta.
Majalisar ta ce duk wanda aka samu da laifi a yanke masa hukunci ba tare da la’akari da girman matsayinsa ba.
Wannan matakin ya biyo bayan kudurin da dan majalisa Faruk Musa Dosara ya gabatar a jiya.
Yana nuna takaicinsa kan yadda aka sace ‘yan matan makarantar Jangebe da ke karamar hukumar Talata Mafara a Zamfara.