Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa ta bukaci Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jihar Nasarawa da su samar da kayan agaji ga wadanda bala’in ambaliyar ruwa ya shafa a jihar.
Wannan, majalisar ta ce, hakan zai rage wahalhalun da suke ciki, tare da inganta yanayin rayuwarsu, da kuma ci gaban jihar baki ɗaya.
Kakakin majalisar, Alhaji Ibrahim Balarabe-Abdullahi, ya yi wannan kiran ne a yayin da yake karanta kudirin majalisar bayan Mista John Osewu (APC), memba mai wakiltar mazabar Doma ta Kudu, ya gabatar da batun a cikin batutuwa masu muhimmanci a yayin zaman da ake yi ranar Litinin a Lafiya.
Balarabe -Abdullahi ya kuma bukaci al’ummomin kusa da kogi da ke fadin jihar da su yi biyayya ga shawarar da kwararru da gwamnatoci a kowane mataki ke bayarwa kan bukatar su koma tsandauri.
“Bari na yabawa Honorabul John Osewu saboda fito da wannan lamari mai mahimmanci a wannan lokaci da kuma jawo hankalin gwamnati akan abin da ke faruwa a mazabarsa.
”Ina kuma godiya ga Honorabul Mohammed Okpoku da Honorabul David Maiyaki saboda gudummawar da suka bayar. Ina godiya da ku duka.
“maganin matsalar shi ne amsa kiran da Majalisar ta yi ga hukumomin gwamnati da abin ya shafa da su taimaka wa wadanda bala’in ambaliyar ruwa ya rutsa da su a fadin jihar.
“Muna kira ga hukumar wayar da kai ta kasa (NOA) da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Nasarawa (NASEMA) da su tashi tsaye su yi hakan ta hanyar wayar da kan mutanen mu da su bi shawarar da gwamnati ta bayar na kaura daga yankunan dake da hatsari zuwa wuraren tsaro don gujewa asarar rayuka da ta dukiyoyi, ”inji shi.