Majalisar dokokin Kano ta tantance tare da amincewa da nadin Aminu Ibrahim Tsanyawa, a matsayin kwamishina kuma mamba a majalisar zartaswa ta jihar Kano.
Majalisar ta amince da shine a zamanta na Ranar Talatar karkashin jagorancin shugaban majalisar Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari.
A zaman majalisar na jiya Litinin ne gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya aike da sunan Aminu Ibrahim Tsanyawa, don tantance shi cikin mutane goma da za a nada kwamishinoni don maye gurbin wadanda suka ajiye aiki domin yin takara a zaben badi dake tafe.
KARANTA ANAN: Ma’aikata Sun gudanar da Zanga Zangar Rashin Ganin Albashin Shekaru 5
Aminu Ibrahim Tsanyawa dai shine tsohon kwamishinan lafiya da ya sauka don shiga zaben fidda gwani, inda ya nemi takarar majalisar tarayya mai wakiltar kunci da Tsanyawa.
Sai dai rashin samun tikitin takarar yasa kuma gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya sake tura sunan sa don nada shi a matsayin kwamishina, wanda kuma majalisar ta amince dashi a zamanta na Talatar nan.
Da yake jawabi bayan tantance shi Aminu Ibrahim Tsanyawa, ya ce zai dora kan ayyukan ci gaba da ya faro don ciyar da jihar Kano gaba.
Aminu Ibrahim Tsanyawa, ya kuma ce wannan karon zasu fi maida hankalin ga bangarorin da suka fi fuskantar matsala domin magance su.
A wani labarin kuma: Malaman Jami’ar FUDMA Sun Shirya Tsunduma Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani
Kungiyar malaman jami’o’i reshen Dutsin-Ma ta yi kira ga mambobin kungiyar da su shiga yajin aiki na dindindin idan har gwamnatin tarayya ta ci gaba da yin watsi da bukatun kungiyar.
‘Yan kungiyar ASUU a jami’ar sun kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta “dawo kan sabon daftarin yarjejeniyar na 2009 FGN/ASUU a matsayin nuni na gaskiya.”