Kungiyar malaman jami’o’i reshen Dutsin-Ma ta yi kira ga mambobin kungiyar da su shiga yajin aiki na dindindin idan har gwamnatin tarayya ta ci gaba da yin watsi da bukatun kungiyar.
‘Yan kungiyar ASUU a jami’ar sun kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta “dawo kan sabon daftarin yarjejeniyar na 2009 FGN/ASUU a matsayin nuni na gaskiya.”
‘Yan kungiyar ASUU sun cimma wannan matsaya ne bayan taron da suka gudanar a harabar jami’ar da ke Dutsin-ma a ranar Litinin.
An gabatar da kwafin kudurorin da aka cimma yayin taron ga manema labarai a yau Talata.
KARANAN ANAN: Najeriya Na Bukatar Shugabanni Da Zasu Tabbatar da Ita a Ƙasa Ɗaya – Okowa
Shugaban kungiyar reshen reshen jami’ar Jibrin Shagari da Sakatare Mzungu Ignatius ne suka sanya hannu kan sanarwar.
“Rashin ganin gwamnati ta magance matsalolin kamar yadda aka bayyana a sama, ya kamata kungiyar ta ci gaba da yajin aikin gaba daya.
Kungiyar reshen jami’ar tana kira ga Gwamnatin Tarayya da ta dawo kan sabon daftarin yarjejeniyar na 2009 FGN/ASUU da kuma duba rahoton kwamitin sulhu domin nuna gaskiya.”
A halin da ake ciki, har yanzu al’amura a FUDMA da Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’dua da ke Katsina sun ci tura har zuwa safiyar Talata bayan yajin aikin ASUU.
A wani labarin kuma: Atiku Yayi Karin Haske Kan Batun Mika Ragamar Jami’o’in Najeriya Ga Jihohi
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya musanta zancen da ake yadawa cewar zai mayar da jami’o’in kasar nan hannun gwamnonin jihoji.
Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da kakakinsa Paul Ibe ya fitar da yammacin ranar Litinin, tare da rabawa manema labarai.