Majalisar dokokin jihar Katsina ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta gyara makarantu biyu da suka lalace a karamar hukumar Sabuwa na jihar.
Majalisar ta yi wannan kiran ne a ranar Talata, yayin zaman majalisar, biyo bayan wani kudiri da Alhaji Ibrahim Danjuma, (APC Sabuwa) mai wakiltar mazabar Sabuwa ya gabatar.
A cewar Danjuma, makarantun da abin ya shafa su ne Makarantun Sakandaren Gwamnati guda biyu da ke Sabuwa da Dungun Mu’azu a karamar hukumar.
Ya ci gaba da bayanin cewa kiran gyaran makarantun ya zama dole saboda mummunan halin da suke ciki wanda, ya bayyana a matsayin “abin kunya”.
“Lokacin da muka ziyarci makarantun, yanayin ya munana matuka ta yadda dalibai suke samun darussa
a kasa saboda rashin kujeru da tebura.
“Wasu azuzuwan ba su da rufi a yayin da ɗaliban ke samun wurin buya a wani wuri, yayin da suke samun darussa a lokacin damina.
“Wannan halin ya tilastawa mutanen yankin yin magana da ni a kan lamarin domin su jawo hankalin gwamnatin jihar da kubutar da barazanar karatun ‘ya’yansu.
“Kamar yadda kuka sani, ɗalibai ba za su iya fahimtar komai a makaranta ba idan babu ingantaccen yanayin koyo. Duk da mummunan yanayin makarantun su, duk da haka, yaran har yanzu suna zuwa makarantar saboda suna da sha’awar koyo. ” ya ce.
Don haka, ya yi kira ga gwamnati da ta taimaka wa yaran da ke makarantun da abin ya shafa domin ci gaban ilimi a yankin.
Bayan tattaunawar da ‘yan majalisar suka yi, majalisar ta amince da kudirin tare da yin kira ga gwamna Aminu Masari da ya bayar da umarnin a gyara makarantun.