By Ishaq Dabai
Wata bishiyar da ake kyautata zaton ta cika shekaru 100 a duniya ta faɗi bayan tashin wata guguwar iska mai karfi a yankin Saabo na Oyo, cikin jihar Oyo a ranar Litinin, inda mutane huɗu suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata.
An gano cewa itacen, wanda ke kusa da mashahuriyar kasuwar sai da kayan abinci, ya kuma zama wurin shakatawa ga masu hawan babur, masu motocin bas da masu kasuwanci.
Shugaban Kasuwar Saabo, Oyo, Alhaji Akeebu Alarape, wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin ya bayyana cewa bishiyar ta kasance sama da shekaru 100 a can, ya kara da cewa a lokuta da dama an yi kokarin kashe bishiyar.
Da aka tuntubi, Shugaban ayyukan rundunar Amotekun na Atiba LCDA, Mista Akeem Ojo ya tabbatar da cewa lamarin ya faru da misalin karfe 6 na yammar ranar Litinin.sannan yace“Wata daliba mace dake karatu a Kwalejin Ilimi ta Tarayya dake Oyo, da wata mata da jariri daure a bayanta da kuma wani yaro da take rike da shi aka ciro shi daga karkashin bishiyar.
“Mutum daya ya samu munanan raunuka kuma an kai shi wani asibiti mai zaman kansa a yankin, yayin da babura da kananan motoci da aka ajiye a karkashin bishiyar suka lalace.” Ya kara da cewa kasancewar Amotekun a wurin shine don hana tarzoma da satar kayayyaki a cikin. kasuwa.
Shugaban, Sooro LCDA, Mista Seun Oguntona ya kuma bayyana cewa mutanen da abin ya shafa su ne wadanda ke fatauci a karkashin bishiyar, ya kara da cewa za a koma dasu cikin kankanin lokaci.
Sannan yace mutumin da ya dasa itacen ya mutu kimanin shekaru 30 da suka gabata, ya kara da cewa duk da cewa mutumin yana bauta wa Sango yana raye, makasudin dasa bishiyar shi ne samar wa mutane matsuguni.