Majalisar Wakilan Tarayya ta amince da wata takardar korafi da al’ummar Tibi daga Jihar Binuwe mazauna kasashen ketar ta shigar gaban ta.
Majalisar ta amince da karbar takardar ne a zaman ta na yau talata wanda ya gudan a kwaryar Majalisar.
Kungiyar Mai suna Mzough U Tiv Amerika MUTA a takaice ta mika korafin nata ne kan matsalar tsaro dake faruwa a jihohin Binuwe da Nassarawa da kuma jihar Taraba.
Dan Majalisa mai wakiltar mazabar Gwer ta gabas da Gwer ta Yamma ta jihar Binuwe a majalisar Mark Gbillah shine ya mika takardar koke a wa zaman na yau da kakakin Majalisa Femi Gbajabiamila ya jagoranta.
Ya ce ya yi yakin gabatar da takardar ne la’akari da irin yadda aka fatattaki al’ummar Tibi a jihar Binuwe din daga muhallan su.
“Ba tare da wani rudani ba, tashi ka gabatar da takardar taka kuma za a yi la’akari da ita” Gbajabiamila ke gaya wa dan majalisar.
Idan za a iya tunawa dai Mataimakin Kakakin Majalisar Idris Wase ya sanya kafa ya shure bukatar dan majalisar a wani zama da ya jagoranta a madadin Kakanin majalisar a ranar sha daya ga watan Maris din wannan shekara, inda ya ce yan Najeriya mazauna kasashen ketare ba su da hurumin shiga lamuran da ya shafi Najeriya.