Majalisar wakilai ta kuduri aniyar gudanar da bincike kan batan makamai da alburusai 178,459 a rundunar ‘yan sandan Najeriya kamar yadda rahoton babban mai binciken kudi na tarayya na shekarar 2019 ya bayyana.
Kudurin ya biyo bayan kudirin gaggawa na Muhimmancin Jama’a da Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye, Toby Okechukwu, ya gabatar a ranar Alhamis.
Idan dai za a iya tunawa, babban mai binciken kudi na tarayya ya bayyana cewa sama da 88,000 daga cikin makaman da suka bata akwai bindigogi kirar AK-47 da ‘yan sanda ba za su iya tantance su ba.
Da yake gabatar da kudirin, Okechukwu ya ja hankali kan yadda ake cigaba da yaki da ta’addanci da ‘yan fashi, inda ya nuna cewa wadannan makamai za su iya shiga hannun da ba su dace ba.
Sai dai mataimakin kakakin majalisar Ahmed Idris Wase ya ce kwamitin Adoc da majalisar ta riga ta kafa ya kamata a bar shi ya gudanar da ayyukan da suka shafi laifukan bincike yayin da kwamitin da ke kula da asusun gwamnati ya binciki inda makaman suke kamar yadda ya kamata a aikinsa na tsarin mulki.
Wase, wanda ya ce akwai bayanai da dama da ya ke ajiyewa a ransa, ya ce batun bacewar makamai ba zai takaita ga ‘yan sanda kadai ba.