Yan Fashin daji sun sace dalibai da malamai a Makarantar Firamare a kauyen Rama dake karamar hukumar Birnin Gwari na Jihar Kaduna.
Wasu Mazauna garin sun shaida wa Jaridar Daily Trust cewa lamarin ya ritsa da daliban ne yayin da suke hanyar makaranta da misalin karfe tara na safiyar yau Litinin.
Wani shaidar gani da ido mai Suna Abdulsalam Adam ya ce Yan Fashin dajin sun zo ne a kan babur sama da goma sha biyu.
Shi ma wani mai suna Mai Saje Rama ya bayyana cewa, wani mai suna Haliliu wanda uba ne ga daya daga daliban da aka sace ya ga lokacin suka sanya dan nashi a babur amma babu yadda suka iya.
Muhammadu Birnin Gwari daya daga Mazauna Birnin Gwari ya ce daga cikin Malaman da aka sace har da yan uwan shi biyu masu suna Umar Hassan da kuma Rabiu Salisu Takau.