By Abbas Yakubu Yaura
Makarantun Firamare da na Sakandare na gwamnati da masu zaman kansu a Legas za su koma zango na biyu a zangon karatu na 2021/2022 a ranar Talata 4 ga Janairu shekarar 2022.
Wata sanarwa da Darakta Janar na ofishin tabbatar da ingancin ilimi, Misis Abiola Seriki-Ayeni, ta fitar a ranar Juma’a, ta ce ana sa ran dukkan daliban za su dawo makaranta saboda za a fara gudanar da harkokin ilimi a rana guda.
Darakta-Janar na yi wa ɗalibai da malaman farin ciki sake dawowa, tare da gargaɗin dukkan shugabannin makarantun da su tilasta bin duk ka’idojin aminci na cutar COVID-19 a cikin jihar.
Shugabannin makaranta su kuma lura cewa hutun tsakiyar wa’adi na zango na biyu shine Alhamis 17th da Juma’a 18 ga Fabrairu, 2022, yayin da makarantu ke rufe wa’adin ranar Juma’a 8 ga Afrilun shekarar 2022.
Misis Seriki-Ayeni, wadda ya umarci daliban kwana dasu koma ranar Litinin 3 ga watan Janairu, 2022 domin shirye-shiryen gudanar da harkokin ilimi, tace ofishin tabbatar da ingancin ilimi zai sanya ido kan yadda aka bi ranar da za a koma aiki a Kalandar ta Jihar Legas tare da lura da koyarwar hanyoyin koyo a makarantu.